Demokradiyyar Congo: Ana Ci Gaba Da Samun Tashin Hankali A Yankin Ituri
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28999-demokradiyyar_congo_ana_ci_gaba_da_samun_tashin_hankali_a_yankin_ituri
Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Demokradiyyar Congo Henri Mova ne ya sanar da haka, yana mai nuna damuwarsa akan lamarin
(last modified 2018-08-22T07:01:33+00:00 )
Mar 12, 2018 05:51 UTC
  • Demokradiyyar Congo: Ana Ci Gaba Da Samun Tashin Hankali A Yankin Ituri

Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Demokradiyyar Congo Henri Mova ne ya sanar da haka, yana mai nuna damuwarsa akan lamarin

Radiyon kasa da kasa na Faransa ya ambato Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Demokradiyyar Congo yana cewa; Wasu mutane dauke da makamai suna kai hare-hare tare da kone gidaje da gonakin mutanen Ituri.

Tuni ministan harkokin cikin gidan, ya fara ganawa da bangarori daban-daban na al'ummar yankin domin samo mafita. Har ila yau ministan ha sanar da gabatar da mutane 53 a gaban kotu, saboda tuhumarsu da ake yi da hannu a tashin hankalin.

Yankunan gabaci da kuma arewa maso gabacin kasar ta Demokradyyar Congo na fama da rikice-rikice fiye da shekaru 20 da su ka gabata.