Dalilan Ci Gaba Da Bullar Rikicin Kabilanci A Yankin Kudancin Kasar Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29242-dalilan_ci_gaba_da_bullar_rikicin_kabilanci_a_yankin_kudancin_kasar_libiya
Rikicin kabilanci a garin Sabha da ke kudancin Libiya ya lashe rayukan mutane tare da jikkata wasu adadi mai yawa baya ga tilastawa wasu fiye da 4,500 tserewa daga muhallinsu.
(last modified 2018-08-22T07:01:35+00:00 )
Mar 20, 2018 03:08 UTC
  • Dalilan Ci Gaba Da Bullar Rikicin Kabilanci A Yankin Kudancin Kasar Libiya

Rikicin kabilanci a garin Sabha da ke kudancin Libiya ya lashe rayukan mutane tare da jikkata wasu adadi mai yawa baya ga tilastawa wasu fiye da 4,500 tserewa daga muhallinsu.

A cikin 'yan shekarun baya-bayan nan yankin kudancin Libiya yana fama da matsalolin tashe-tashen hankula fiye da sauran yankunan kasar sakamakon bullar rikicin kabilanci. A cikin watan Oktoban shekara ta 2016 yankin ya yi fama da rikicin kabilanci tsakanin kabilar Auladu-Sulaiman da na Tubu da suke goyon bayan tsohon shugaban kasar Mu'ammar Gaddafi, inda aka samu hasarar rayuka dana dukiyoyi a tsakaninsu. Hakika sake bullar wani sabon rikicin tsakanin bangarorin biyu tun a ranar 4 ga watan Fabrairun wannan shekara ta 2018, an samu bullar hasarar rayuka tare da jikkatan mutane masu yawa musamman fararen hula daga cikinsu, baya ga raba mutane fiye da 4,500 da muhallinsu.

Tushen bullar tashe-tashen hankula tsakanin al'ummar Libiya baya rasa nasaba da sabanin kabilanci da al'adu musamman a halin zamantakewarsu, inda irin wannan masifa tafi kamari a yankunan da suke kudancin kasar, kuma a halin yanzu haka ana ci gaba da fafatawa tsakanin kabilar Auladu-Sulaiman da na Tubu, kuma rikicin ya kunno kai ne sakamakon kashe dan kabilar Tubu da dakarun runduna ta shida ta gwamnatin hadin kan kasar ta Libiya karkashin jagorancin fira minista Fayyaz Assarraj suka yi, kuma 'yan kabilar Auladu-Sulaiman ne ke jagorancin rundunar lamarin da ya fusata 'yan kabilar Tubu suka dauki matakin maida martani ta hanyar kaddamar da hari kan cibiyar rundunar ta shida da ke garin Sabha.

Baya ga rikicin kabilanci a Libiya, matsalar shugabancin ma tana taka gagarumar rawa a fagen haifar da tashe-tashen hankula a kasar. Tun a watan Agustan shekara ta 2014 zuwa yanzu gwamnatoci biyu ne ke jagoranci a kasar ta Libiya, inda gwamnatin hadin kan kasa karkashin jagorancin fira minista Fa'iz As-Sarraj ke da cibiya a birnin Tripoli fadar mulkin kasar, sannan tsohuwar gwamnatin kasar karkashin jagorancin Abdullahi al-Thani da ke samun goyon bayan babban kwamandar rundunar sojin kasar Janar Khalifa Haftar ke da cibiya a garin Tobruk a gabashin kasar ta Libiya, kuma kabilar Tubu tana goyon bayan gwamnatin Tobruk ce yayin da kabilar Aulad-Sulaiman ke goyon bayan gwamnatin Tripoli.

Har ila yau matsalar rashin rundunar sojin kasa a garin Sabha ya sanya kabilun yankin ne ke kula da harkokin tsaron garin lamarin da ke janyo sabani a tsakaninsu da ke kai ga bullar tashe-tashen hankula. Kamar yadda matsalar talauci a shiyar kudancin kasar ta Libiya ke kara taka gagarumar rawa a fagen habaka rashin zaman lafiya da tsaron yankin.