Saliyo: "Yan Adawa Sun Zargi Gwamnatin Da Kokarin Haddasa Hargitsi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29388-saliyo_yan_adawa_sun_zargi_gwamnatin_da_kokarin_haddasa_hargitsi
Dan takarar shugabancin kasar Saliyo mai wakiltar jam'iyyar hamayya ya ce gwamnatin kasar tana son hana a yi zabe zagaye na biyu
(last modified 2018-08-22T07:01:36+00:00 )
Mar 26, 2018 14:33 UTC
  • Saliyo:

Dan takarar shugabancin kasar Saliyo mai wakiltar jam'iyyar hamayya ya ce gwamnatin kasar tana son hana a yi zabe zagaye na biyu

Dan takarar shugabancin kasar, Julius Maada Bio ya bayyana haka ne a wani taron manema labaru da ya gabatar a babban birnin kasar Free Town, yana mai yin kira ga mutanen kasar da su gudanar da Zanga-zangar lumana domin nuna kin amincewa da shirin gwamnatin.

Julius Maada Bio ya ce; Abin da ya sa mahukuntan kasar ba su son a yi zabe zagaye na biyu, shi ne sanin da suka yi akan sakamakon da za a samu.

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai Kotun Kolin kasar ta Saliyo ta dakatar da gudanar da shirye-shirye domin zagaye na biyu na zabe, bisa karar da jam'iyya mai mulki ta shigar na zargin yin magudi a zagaye na farko.