An Sanar Da Sabon Fira Ministan Kasar Habasha
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29422-an_sanar_da_sabon_fira_ministan_kasar_habasha
A jiya talata ne kawancen jam'iyyun da ke mulki a kasar ta Habash ya sanar da sunan Abiye Ahmed a matsayin wanda zai maye gurbin Hailemarim Desalegn da ya yi murabus.
(last modified 2018-08-22T07:01:37+00:00 )
Mar 28, 2018 04:53 UTC
  • An Sanar Da Sabon Fira Ministan Kasar Habasha

A jiya talata ne kawancen jam'iyyun da ke mulki a kasar ta Habash ya sanar da sunan Abiye Ahmed a matsayin wanda zai maye gurbin Hailemarim Desalegn da ya yi murabus.

Kawancen Jam'iyyun da ke  mulki  a Habasha ya kunshi al'ummun Tajrai da Oromo sai kuma Amhara da kungiyar demokradiyya ta mutanen kudancin Habasha.

Kawancen jam'iyyun yana gudanar da taro sau biyu a kowace shekara, domin sanar da sabon shugaba da kuma wanda zai hau kujerar fira minista.

A ranar 15 ga watan Febrairu na wannan shekarar ne dai Heilemariam Desalegn ya yi murabus daga kan mukaminsa na Fira minista. Sai dai ya sanar da cewa zai ci gaba da rike mukamin nasa har zuwa lokacin da kawancen da ke mulki a kasar ya amince da murabus din nashi.

Kasar ta Habasha tana fuskantar dambaruwar siyasa saboda zanga-zangar da wasu kabilun kasar suke yi dangane da matsalar gonakin noma.