Jami'an Tsaron Tanzaniya Sun Kama Madugun 'Yan Adawar Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29432-jami'an_tsaron_tanzaniya_sun_kama_madugun_'yan_adawar_kasar
Ma'aikatar shari'ar Tanzaniya ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun kame madugun 'yan adawar Tanzaniya.
(last modified 2018-08-22T07:01:37+00:00 )
Mar 28, 2018 08:11 UTC
  • Jami'an Tsaron Tanzaniya Sun Kama Madugun 'Yan Adawar Kasar

Ma'aikatar shari'ar Tanzaniya ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun kame madugun 'yan adawar Tanzaniya.

Ma'aikatar shari'ar Tanzaniya ta sanar da cewa: Jami'an tsaron Tanzaniya sun kame madugun 'yan adawar kasar Freeman Mbowe tare da wasu mukarrabansa guda biyar a jiya Talata kan zargin kokarin kunna wuta rikici da tarzoma a kasar.

Majiyar ma'aikatar shari'ar ta kara da cewa: Ana zargin Freeman Mbowe na jam'iyyar Party for Democracy and Progress da yin furucin tada tarzoma a lokacin gudanar da zanga-zangar adawa a ranar 16 ga watan Fabrairu a kokarin da suke yi na kawo karshen gwamnatin John Magufuli.