An Hallaka Mutane 10 A Gabashin Kwango
Kimanin fararen hula 10 ne da wani Mutum da ake zarkin ya nada alaka da 'yan ta'awaye , suka hallaka a wani rikici da ya wakana a garin Beni na gabashin demokaradiyar kwango
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto majiyar tsaron jamhoriyar demokaradiyar Kwango na cewa kimanin mutane 10 da kuma wani dan tawaye guda ne suka rara rayukansu a yayin fafatawa tsakanin sojoji da 'yan tawayen Allied Democratic Forces (ADF) dake gabashin kasar.
Tun a watan janairu ne sojojin kasar Kwangon suka kadamar da farmaki kan 'yan tawayen na (ADF) a gabashin kasar, to saidai wannan farmaki na ci gaba da lagume rayukan fararen hula mazauna garin Beni da kauyukan dake kewaye da shi.
'Yan tawayen Allied Democratic Forces (ADF), 'yan adawar shugaba Yoweri Museveni ne da suka kafa sansanisu a jahar Kivo ta arewa dake gabashin jamhoriyar demokaradiyar kwango tun a shekarar 1995, a shekarar 2014 sun kashe dariruwan fararen hula a yankin na Beni.
A watan Dicembar shekarar 2017 din da ta gabata, an zargi 'yan tawayen da kashe dakarun wanzar da zaman lafiya 'yan kasar Tanzaniya 15.
A ranar Talatar da ta gabata, kwamitin tsaron MDD ya amince da wani sabon kudiri na karfafa dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar a kasar Demokaradiyar Kwango.