Dambarwar Siyasa Tana Ci Gaba Da Yin Kamari A Guinea Conakry
Rikicin siyasa tsakanin 'yan adawar Guinea Conakry da gwamnatin kasar yana ci gaba da yin kamari a cikin 'yan kwanakin nan.
Matakin da gwamnatin Guinea Conakry ta dauka na kin amincewa da bukatar 'yan adawar kasar ta kafa wani kwamitin bincike da zai dauki alhakin bankado musabbabin kisan gillar da aka yi wa masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar a 'yan watannin baya-bayan nan, hakan ya kara janyo bullar wata sabuwar dambaruwar siyasa a kasar.
A cikin 'yan watannin baya-bayan nan al'ummar Guinea Conakry sun gudanar da zanga-zanga a sassa daban daban na kasar a kan matsaloli daban daban amma sai jami'an tsaro suka yi amfani da karfi kansu fiye da kima lamarin da ya janyo hasarar rayuka tare da jikkata masu da dama gami da tsare wasu a gidajen kurkuku.