Moroko Ta Kai Karar "Polisario" A Gaban Majalisar Dinkin Duniya
Ministan harkokin wajen kasar Moroko ya kira yi MDD da Aljeriya da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu domin hana "Polisario" ci gaba da kai hari a yankin yammacin sahara
Bayan ganawar da ministan harkokin wajen kasar Moroko Nasir Bu Ridha ya yi da babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Antinio Gutteress, ya fadawa manema labaru cewa: Ya mika wa Gutteress rubutacciyar wasika daga sarkin Moroko Muhammadu Na Shida da a ciki ya ce; matukar kwamitin tsaro bai yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa ba, to Moroko za ta dauki mataki.
Ministan harkokin wajen Moroko ya kuma ce abin da kungiyar ta Polisario ta yi, barazana ce ga tsagaita wutar yaki da kuma keta kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.
Bugu da kari, Morokon ta bakin ministan harkokin wajenta ta zargi kasar Aljeriya da taimakawa kungiyar Polisario da kudade da kuma kariya ta diplomasiyya.
Kasar Moroko ta kwace iko da yankin yammacin Sahara ne a 1975.