An Kashe Mutane 4 A Gabancin Kasar Demokradiyyar Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29814-an_kashe_mutane_4_a_gabancin_kasar_demokradiyyar_congo
Sojojin gwamnatin kasar ta Demokradiyyar Congo ne su ka sanar da kai farmaki akan wata kungiya ta masu dauke da makamai tare da kashe shugabanta da kuma masu gadinsa
(last modified 2018-08-22T07:01:41+00:00 )
Apr 11, 2018 03:37 UTC
  • An Kashe Mutane 4 A Gabancin Kasar Demokradiyyar Congo

Sojojin gwamnatin kasar ta Demokradiyyar Congo ne su ka sanar da kai farmaki akan wata kungiya ta masu dauke da makamai tare da kashe shugabanta da kuma masu gadinsa

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ce an kai harin ne a gundumar Kivo ta Arewa da yake fama da tashe-tashen hankula. Sojojin sun kai harin ne a garin Uvira a kusa da iyakar kasar Brundi.

Da akwai kungiyoyi masu yawa da suke dauke da makamai a yankin na Kivo da su ka hada da kungiyar Kara-kara.

Tare da cewa da akwai sojojin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar, sai dai kungiyoyin masu dauke da makamai na cikin gida da kuma kasashen makwabta suna ci gaba da kai hare-hare.