An Karyata Jita-Jitar Mutuwar Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Libya Khalifa Haftar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29902-an_karyata_jita_jitar_mutuwar_babban_hafsan_hafsoshin_sojin_libya_khalifa_haftar
Rahotanni daga kasar Libya na cewa jami'an gwamnatin kasar sun karyata jijitar da ake yadawa kan mutuwar Khalifa Haftar.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Apr 14, 2018 13:45 UTC
  • An Karyata Jita-Jitar Mutuwar Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Libya Khalifa Haftar

Rahotanni daga kasar Libya na cewa jami'an gwamnatin kasar sun karyata jijitar da ake yadawa kan mutuwar Khalifa Haftar.

Kamfanin dillancin labaran farsa ya bayar da rahoton cewa, babban mashawarcin Haftar Fadil Aldib ya bayyana cewa, babu gaskiya a cikin dukkanin rahotannin da aka yi ta yadawa kan mutuwar tasa.

Ya ce Janar haftar bai yi tafiya zuwa Jordan ba, amma ya yi tafiya zuwa Faransa domin duba lafiyarsa, kuma yana samun sauki bayan aikin da aka yi masa, kuma nan ba da jimawa ba zai komo kasar Libya domin ci gaba da ayyukansa.