Manyan Hafsoshin Sojan Afirka Na Taro A Najeriya
Manyan hafsoshin sojin kasa daga sassa daban daban na Nahiyar Afrika sun fara wani taro kan sha'anin tsaro yau a Abuja babban birnin Najeriya karkashin jagorancin Amurka da nufin hada hannu tsakanin kasashen don yaki da ayyukan ta'addanci.
A cewar Amurka, taron zai taimaka matuka ta yadda kasashen za su hada hannu don kammala fatattakar kalubalen tsaron da kezama babbar barazana ga nahiya ta Afirka
Hafsoshin sojin kasa daga kasashen Angola Kamaru Masar Kenya da kuma Rwanda za su yi musayar bayanai kan yadda za a shawo kan matsalar tsaron da ya kunshi ayyukan ta'addanci kungiyar Al-shabab a gabashin nahiyar da kuma na kungiyar Boko haram a yammaci.
Kafin a korarshi daga bakin aiki a watan Maris da ya gabata, sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya gudanar da wata ziyara a kasashen Nahiyar 5 da nufin nuna goyon bayan kasar kan ci gaba da yaki da ayyukan ta'addanci.
Ko a baya-bayan nan ma Amurkan ta jagoranci wani atisayen soji daya kunshi dakaru daga kasashe 26 a jamhuriyar Nijar da nufin fatattakar ayyukan ta'addanci a yankin Sahel.