Demokradiyyar Congo: An Kori Alkalai 200 Daga Aiki
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30044-demokradiyyar_congo_an_kori_alkalai_200_daga_aiki
Radiyon kasa da kasa na Faransa ne ya bada labarin cewa shugaba Joseph Kabila ya ba da umarnin korar alkalan da suke a matsayin kaso 6 % na dukkanin alkalan kasar
(last modified 2018-08-22T07:01:43+00:00 )
Apr 17, 2018 08:40 UTC
  • Demokradiyyar Congo: An Kori Alkalai 200 Daga Aiki

Radiyon kasa da kasa na Faransa ne ya bada labarin cewa shugaba Joseph Kabila ya ba da umarnin korar alkalan da suke a matsayin kaso 6 % na dukkanin alkalan kasar

Daga cikin alkalan da korar ta shafa da akwai masu alaka da jam'iyyun siyasa da kuma dangi ko iyayen wasu jami'an gwamnati.

Tun a baya, ma'aiaktar shariar kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta bakin babban mai shigar da kara, Alexis Thambe Mwamba ya zargi wasu daga cikin alkalan kasar da cin hanci da karbar rashawa.

Sai dai babu wani cikakken bayani ko karar da aka yi wa alkalan a wannan karon tana da alaka da batun cin hanci da rashawar.