Rwanda: Ambaliyar Ruwan Sama Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama
Majiyar gwamnatin Rwanda ta ce fiye da mutane 200 su ka mutu da kuma jikkata saboda ambaliyar ruwan sama a cikin garuruwan kasar
Radiyon Sawahili na muryar jamhuriyar musulunci ta Iran ya ba da labarin cewa, ruwan sama da bakin kwarya da aka rika samu a cikin kasar a watanni biyu na bayan nan ya ci ran mutane 41 da kuma jikkata wasu 162.
Hukuma mai kula da bala'oi na dabi'a a kasar Rwanda ta fitar da bayani wanda a ciki ta kira yi mazauna yankunan da ake samun ambaliyar da su fice daga gidajensu, kamar kuma yadda ta yi suka ga hukuma mai hasashen sauyin yanayi saboda kuskuren hasashe.
Al'ummar kasar suna dora asarar rayukan da ake samu akan mahukuntan kasar na kasa fusakntar matsalar daga tushenta.