An Sauya Sunan Kasar Swaziland Zuwa eSwatini
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30122-an_sauya_sunan_kasar_swaziland_zuwa_eswatini
Sarkin kasar ne Mswati III ya sanar da sauya kasar suna a yayin bikin cikarta shekaru 50 da samun 'yanci
(last modified 2018-08-22T07:01:43+00:00 )
Apr 20, 2018 07:25 UTC
  • An Sauya Sunan Kasar Swaziland  Zuwa eSwatini

Sarkin kasar ne Mswati III ya sanar da sauya kasar suna a yayin bikin cikarta shekaru 50 da samun 'yanci

sarki Mswati III  ya ce mutane da dama suna rudewa da kasa banbance tsakanin sunan kasarsa  Swaziland da kasar  Switzerland.

Kasar ta sami 'yanci ne daga mulkin mallakar Birtaniya a 1968.

Wannan dai ba shi ne karon farko da wata kasa a nahiyar Afirka ta sauya sunanta ba, inda a baya kasashe da dama su ka yi hakan kamar Malawi da Botswana da Zimababwe.