Yansanda Da Yan Adawa Sun Kara A Kasar Madagaska
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30166-yansanda_da_yan_adawa_sun_kara_a_kasar_madagaska
Yansanda ya yan adawa a birnin Antananarivo na kasar Madagascar sun kara a lokacinda yan sanda suka yi kokarin tarwatsa wata zanga-zangar lumana wacce yan adawar suka shirya don nuna rashin amincewarsu da kafa wasu dokoki wadanda zasu hada yan takararsu tsayawa zaben shugaban kasa nan gaba a cikin wannan shekara.
(last modified 2018-08-22T07:01:44+00:00 )
Apr 21, 2018 14:35 UTC
  • Yansanda Da Yan Adawa Sun Kara A Kasar Madagaska

Yansanda ya yan adawa a birnin Antananarivo na kasar Madagascar sun kara a lokacinda yan sanda suka yi kokarin tarwatsa wata zanga-zangar lumana wacce yan adawar suka shirya don nuna rashin amincewarsu da kafa wasu dokoki wadanda zasu hada yan takararsu tsayawa zaben shugaban kasa nan gaba a cikin wannan shekara.

Tashar talabijon ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa daruwan yan adawa ne, daga ciki har da yan majalisar dokokin kasar ta Madagascar suka fito kan tituna a safiyar yau asabar don nuna rashin amincewarsu da wasu dokokin da majalisar dokokin kasar ta amice da su, wadanda a ganinsu wani shinge ne suka dorawa dan takararsu, kuma tsohon shugaban kasar Mark Ravalomanana tsayawa takarar shugabancin kasar .

Wani dan majalisar dokokin kasar wanda ya ke cikin masu zanga-zangar, paul Bert Rahasimanana, ya ce dole shugaban kasar Hery Rajaonarimampianina ya sauka don suna aikinsu ya aiko masu, a matsayinsu na yan majalisa amma sai ya aiko masu da yan sanda wadanda suka fesa masu teargas. Majiyar yansanda ta tabbatar da mutuwar mutum guda da kuma jikita wasu 16.