Macron Da Al-sisi Sun Tattauna Ta Wayar tarho Kan Rikicin Syria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30178-macron_da_al_sisi_sun_tattauna_ta_wayar_tarho_kan_rikicin_syria
Shugabannin kasashen Faransa da Masar sun tattauna ta wayar tarho kan batun rikicin kasar Syria.
(last modified 2018-08-22T07:01:44+00:00 )
Apr 22, 2018 02:14 UTC
  • Macron Da Al-sisi Sun Tattauna Ta Wayar tarho Kan Rikicin Syria

Shugabannin kasashen Faransa da Masar sun tattauna ta wayar tarho kan batun rikicin kasar Syria.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya tuntubi shugaban kasar Masar Abdylfattah Al-sisi ta wayar tarho a jiya, inda suka tattauna kan batun halin da ake ciki dangane da rikicin kasar Syria.

Macron dai ya bayyana wa Al-sisi damuwarsa kan halin da ake ciki a Syria, ya kuma wanke kansa dangane da biye wa Amurka da Birtaniya da ya yi wajen kai wa kasar Syria harin soji da cewa, abin da suka yi yana bisa ka'ida kuma bai saba wa dokokin kasa da kasa ba.

A nasa bangaren Abdulfattah Sisi wanda tun farko ya yi Allawadi da harin da Amurka da Birtaniya gami da Faransa suka kaddamar kan Syria, ya bayyana wa Macron cewa, wannan mataki ya kara dagula lamurra a hankoron da ake yi na ganin an warware matsalar ta hanyar siyasa da fahimtar juna.

Emmanuel macron da Theresa May firayi ministan Birtaniya, suna fuskantar kakkausar suka a cikin gida, dangane da yadda suka yi gaban kansu wajen biye wa Trump, a harin da gwamnatinsa ta jagoranta kan Syria.