Masar Za Ta Bude Kofar Rafah Na Kwanaki Uku.
Hukumomin birnin Alkahira sun sanar a jiya juma'a cewa a yau assabar za su bude hanyar Rafah na tsahon kwanaki uku domin kai kawon mazauna yankin Zirin Gaza na Palastinu cikin kasar
A halin da ake cikin akwai duban daliban jami'a, marassa lafiya da kuma 'yan kasashen waje mazauna yankin zirin Gaza dake jiran buda hanya, duk da cewa lokacin da gwamnatin Masar take bayarwa na kai kawo ba zai wadatar ba, to hakan wata dama ce da mazauna yankin zirin gazar za su samu dama shiga kasar ta Masar domin tanadin ababen da suke bukata, kamar magani da kuma ababen masurifi, har ila yau da kuma shigar da marasa lafiya cikin kasar domin yi musu magani.
Masu sharhi na ganin cewa shekarar 2017 din da ta gabata ita ce shekara mafi muni na ynayin buda hanyar ta Rafah, idan aka kwatamta da shekarun da suka gabata, domin a cikin shekarar 2017 din da ta gabata an buda kofar ne kwanaki 35 kacal.
Hanyar Rafah, ita ce hanyar kasa da al'ummar yankin zirin Gaza na Palastinu ke amfani da ita wajen shiga kasar Masar, kuma a shekarar 2013 ne gwamnatin kasar Masar ta rufe ta, kuma ba a bude wannan hanya sai kawai za a shigar da kayan gajin gaggauwa cikin yankin na Gaza.