Wani Ma'aikacin Hako Da Ma'adinai Ya Hallaka A Johannesburg
Girgizar kasar ta auku a gefen birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu ya yi sanadiyar mutuwar wani ma'aikacin hako da ma'adinan zinari tare da bacewar wasu biyar na daban.
Cikin wata sanarwa da James Wellsted kakakin Kamfanin hako da ma'adinan zinari na Sibanil Steel Water ya fitar ya ce girgizar kasar ta auku ne yayin da ma'aikatan dake karkashin kasa da yai kilomita uku, kuma ya zuwa yanzu dakarun kai agaji da ceto sun samu nasarar ceto da dama daga cikin ma'aikatan, saidai guda daga cikin su ya rasa ransa sakamakon mumunan raunin da ya samu.
Rahotani sun ce zuwa karshen daren jiya alhamis akwai ma'aikata 8 a karkashin kasar.
Dakarun Agajin sun tabbatar da gano wurin da uku daga cikin ma'akatan uku, amma biyar har ya zuwa lokacin sanarwar ba a gano takamaiman wurin da suke ba.