Libiya:An Kashe Sojojin Khalifa Haftar 7 A Gabashin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30534-libiya_an_kashe_sojojin_khalifa_haftar_7_a_gabashin_kasar
An hallaka wasu sojoji masu biyayya da janar Khalifa haftar 7 a garin Derna dake gabashin kasar Libiya.
(last modified 2018-08-22T07:01:47+00:00 )
May 04, 2018 08:59 UTC
  • Libiya:An Kashe Sojojin Khalifa Haftar 7 A Gabashin Kasar

An hallaka wasu sojoji masu biyayya da janar Khalifa haftar 7 a garin Derna dake gabashin kasar Libiya.

Wata majiyar tsaron kasar Libiya ta sanar da cewa a wani farmaki da sojojin dake biyayya da Khalifa Haftar suka kaiwa mayakan Majalisar Shura na mayakan Derna dake gabashin kasar, Sojoji 7 suka hallaka yayin da wasu 6 na daban suka jikkata.

A cewar Faraj Almabri daya cikin manyan jami'an tsaron kasar ta Libiya kuma na kusa da Janar Haftar, sojojinmu suna ci gaba da samun nasara kan mayakan na kungiyar mujahideen kuma a halin da ake ciki, mun tsarkake anguwani da dama a garin na Derna.

Garin Derna dake gabashin kasar ta Libiya ya kwashe lokaci mai tsaho yana karkashin ikon kungiyar ta'addancin nan ta Mujahidin mai alaka da kungiyar Alqa'ida.