An Kafa Gwamnatin Rikon Kwarya A Gabon
Kwanaki uku da murabus din gwamnati bisa umarnin kotun kare kundin tsarin milkin kasar, a jiya juma'a an kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar Gabon.
Gwamnatin rikon kwaryar za ta tafiyar da al'amuran kasar har lokacin da za a gudanar da zaben 'yan Majalisa da kuma kafa sabuwar gwamnati.
Tun a shekarar 2016 ne ya kamata a gudanar da zaben 'yan Majalisar, saidai saboda wasu matsaloli aka yi ta daga zaben, lamarin da ya sanya kotun kare kundin tsarin kasar ta rusa majalisar dokoki tare da umartar gwamnati ta yi murabus.
A ranar talatar da ta gabata ce, Piraministan kasar Gabon Emmanuel Issoze Ngondet ya amsa umarnin kotun kare kundin tsarin milkin kasar, inda ya meka takardar murabus din gwamnatinsa ga shugaban kasar Ali Bongo Ondimba.