An Kafa Dokar Ta Baci Akan Cutar Ebola A Kasar Habasha.
May 13, 2018 07:31 UTC
Kasar Habashan ta dauki wannan matakin ne bayan da cutar ta Ebola ta bulla a cikin kasar Demokradiyyar Congo
Gwamnatin kasar ta Habasha ta sanar da matakin ne a jiya asabar ta hanyar tsaurara matakai na kiwon lafiya a filin saukar jiragen sama da sauran iyakokin kasar. Matakin yana nufin hana shigar masu dauke da cutar ta Ebola cikin kasar.
Buu da kari, an tanadi magungunan da za a bai wa wadanda su ka kamu da cutar a cikin fadin kasar, kama daga kan cibiyoyin ba da magani da kuma suaran asibitocin kasar.
Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Demokradiyyar congo ta sanar da mutuwar mutum guda wanda ya kamu da cutar yayin da aka killace wasu mutane 11 da su ka kamu da ita.