Sake Bullar Cutar Ebola A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Ta Janyo Damuwa
May 17, 2018 07:23 UTC
Ma'aikatar lafiya a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta bayyana tsananin damuwarta kan sake bullar cutar Ebola a kasar.
A sanarwar da ma'aikatar lafiya a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta fitar a yau Alhamis ta fayyace cewa: An samu bullar cutar Ebola a garin Mbandaka mai yawan jama'a da suka kai kimanin miliyan guda lamarin da ke matsayin babbar barazana.
Sanawar ma'aikatar lafiya ta kara da cewa: A halin yanzu haka dai an tabbatar da cewar mutane uku ne suka kamu da cutar yayin da aka killace wasu mutane kimanin 40 da ake zargin sun kamu da kwayar cutar, kuma tun bayan sake bullar cutar ta Ebola a kasar mutane 23 ne suka rasa rayukansu.