An Samu Kyautatuwar Alaka A Tsakanin Kasashen Moroko Da Mauritaniya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31024-an_samu_kyautatuwar_alaka_a_tsakanin_kasashen_moroko_da_mauritaniya
Sabon jakadan Moroko ya mika takardar kama aikinsa a kasar Mauritaniya bayan kasashen biyu sun shafe tsawon shekaru shida suna sabani a tsakaninsu.
(last modified 2018-08-22T07:01:52+00:00 )
May 22, 2018 14:44 UTC
  • An Samu Kyautatuwar Alaka A Tsakanin Kasashen Moroko Da Mauritaniya

Sabon jakadan Moroko ya mika takardar kama aikinsa a kasar Mauritaniya bayan kasashen biyu sun shafe tsawon shekaru shida suna sabani a tsakaninsu.

Jaridar Ra'ayul-Yaum ta habarta cewa: Sabon jakadan kasar Moriko Hamid Shabar a Mauritaniya ya gana da ministan harkokin wajen kasar ta Mauritaniya a birnin Nouakchott a jiya Litinin tare da mika masa takardar fara kama aikinsa a kasar.

Tun a shekara ta 2013 aka samu bullar sabani a tsakanin kasashen Moroko da Mauritaniya kan batun yankin Yammacin Sahara, inda Mauritaniya take goyon bayan shirin Majalisar Dinkin Duniya na warware rikicin yankin ta hanyar lumana amma Moroko ta zarge ta da goyon bayan kungiyar gwagwarmayar Polisario mai fafatukar 'yantar da yankin.