Ruwanda Ta Dauki Matakin Kalubalantar Cutar Ebola
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31044-ruwanda_ta_dauki_matakin_kalubalantar_cutar_ebola
Gwamnatin Ruwanda ta dauki matakin rigakafi da kuma kalubalantar cutar Ebola a kasar.
(last modified 2018-08-22T07:01:52+00:00 )
May 23, 2018 07:21 UTC
  • Ruwanda Ta Dauki Matakin Kalubalantar Cutar Ebola

Gwamnatin Ruwanda ta dauki matakin rigakafi da kuma kalubalantar cutar Ebola a kasar.

Bayan billa cutar ebola a jamhoriyar demokaradiyar kwango, gwamnatin kasar Ruwanda ta dauki matakin rigakafi domin kalubalantar  cutar.

Har ila yau gwamnatin ta ja hankulan 'yan kasar da su kiyaye tare kuma daukan mataki a kan duk wata alama da suke da shakku kanta na kamuwa da wannan cuta.

Ma'aikatar kiyon lafiyar kasar ta Ruwanda ta aike da wata tawagar likitoci ta musaman zuwa ga yankin Rubavu dake yammacin kasar dake kusa da iyakar jamhoriyar demokaradiyar kwango.

A karshen shekarar 2013 zuwa 2016, cutar ebola ta kashe mutum sama da dubu 11 da 300 a yammacin Afirka kuma kasashen jamhoriyar demokaradiyar kwango, Liberia, Guinee da  saliyo sune wadanda wannan bala'i yafi ritsawa da su.