Kungiyar Amnesty Ta bukaci Najeriya Ta Binciki Sojojin Da Suka Yi Fyade
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31076-kungiyar_amnesty_ta_bukaci_najeriya_ta_binciki_sojojin_da_suka_yi_fyade
A wani rahoton da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta fitar a wannan Alhamis ta zarki sojojin Najeriya da kuma na sa-kai da ke taimaka ma su wajen yaki da ayyukan Boko Haram, da yi wa mata fyade tare da ba su abinci a matsayin musaya.
(last modified 2019-03-18T02:12:56+00:00 )
May 24, 2018 06:49 UTC
  • Kungiyar Amnesty Ta bukaci Najeriya Ta Binciki Sojojin Da Suka Yi Fyade

A wani rahoton da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta fitar a wannan Alhamis ta zarki sojojin Najeriya da kuma na sa-kai da ke taimaka ma su wajen yaki da ayyukan Boko Haram, da yi wa mata fyade tare da ba su abinci a matsayin musaya.

Rahoton ya ce matsalar ta samo asali ne tun shekara ta 2015, in da sojojin da kuma ‘yan kato da gora, suka raba matan aure da mazajensu, wanda hakan ya jefa matan cikin yanayi na bukatar abinci saboda rashin wadanda za su taimaka musu.

Daraktan kungiyar ta Amnesty a Najeriya Osai Ojigho, ya bukaci shugaban kasar Muhammadu Bubari da ya dauki wannan batu da muhimmanci ta hanyar kaddamar da bincike da kuma hukunta wadanda aka samu da laifi.

Da dama daga cikin mata da ‘yan mata sun shaida wa Amnesty cewa, sojoji da ‘yan kato da gora sun tilasta musu kulla alaka, abin da ke ba da damar lalata da su.