An Kori Jami'an Diblomasiyyar Angola A Birnin Qudus Daga Ayyukansu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31084-an_kori_jami'an_diblomasiyyar_angola_a_birnin_qudus_daga_ayyukansu
Ministan harkokin wajen kasar Angola ya bayyana korar jami'an dibliomasiyyar kasar gudu biyu daga ayyukansu sanadiyyar halattar bukin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Qudus a kwanakin da suka gabata.
(last modified 2018-08-22T07:01:52+00:00 )
May 24, 2018 14:45 UTC
  • An Kori Jami'an Diblomasiyyar Angola A Birnin Qudus Daga Ayyukansu

Ministan harkokin wajen kasar Angola ya bayyana korar jami'an dibliomasiyyar kasar gudu biyu daga ayyukansu sanadiyyar halattar bukin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Qudus a kwanakin da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya nakalto Manuel Domingos Augusto ministan harkokin wajen kasar Angola yana bada wannan sanarwan a yau Alhamis. Augusto ya kara da cewa wadanda korar ta shafa sun hada da Jakadan kasar a HKI da kuma wani daga cikin jami'an diblomasiyyar kasar a HKI. 

A ranar Litinin 14 ga watan Mayun da muke ciki ne gwamnatin kasar Amurka ta dauke ofishin jakadancinta daga birnin Telaviv zuwa birnin Quds ta kuma gayyaci jami'an diblomasiyyar kasashen duniya da dama don halattar bokin da aka gudanar a cikin sabon ofishin jakadancin a birnin. 

Gwamnatin Amurka ta yi haka duk tare da Allahwadai da kasashen da dama a duniya da dama suka, suna ganin hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.