An Kai Hari Kan Ma'aikatan Hako Da Zinari A D/Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31100-an_kai_hari_kan_ma'aikatan_hako_da_zinari_a_d_congo
Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan cibiyar kawo da zinari a gabashin Demokaradiyar Kwango.
(last modified 2018-08-22T07:01:52+00:00 )
May 25, 2018 06:22 UTC
  • An Kai Hari Kan Ma'aikatan Hako Da Zinari A D/Congo

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan cibiyar kawo da zinari a gabashin Demokaradiyar Kwango.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa kimanin mutane biyar ne suka hallaka cikinsu harda jami'an tsaro biyu a wani hari da aka kai cibiyar hako da zinari a gabashin Demokaradiyar Kwango.

Sanarwa ta ce ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu akwai wasu da dama daga cikin ma'aikatan da suka jikkata.

Sama da shekaru 20 kenan da yankunan tsakiya, gabashi da kuma arewa maso gabashin demokaradiyar kwango ke fama da matsalar rashin tsaro.

Kasawar sojojin Kwango da na MDD wajen kalubalantar 'yan tawaye a kwangon, ya kara sanya wanzuwar rashin tsaron a kasar.