Zaizayar Kasa Ta Ci Rayukan Mutum 32 A Kasar Ethiopia
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka fara tun a farkon wannan mako da muke ciki a kasar Ethiopia yayi sanadiyar zaizayewar kasa a wasu yankuna na kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 32
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya habarta cewa tun a farkon wannan mako ne ake zabka ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar Ethiopia, lamarin da ya janyo zaizayewar kasa a wasu yankunan kasar har ta kai ga rasa rayukan mutum 32.
Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu, zaizayar kasar ta janyo hasarar dukiyoyin masu yawa, da kuma jikkatar wasu 17 na daban a ranar lahadi wayewar jiya litinin.
Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da ruwan damuna ya fara sauka a fadin kasar baki daya.
Tuni dai gwamnatin kasar ta sanar da tura jami'an agaji zuwa yankunan da lamarin ya auku domin taimakawa wadanda wannan bala'i ya ritsa da su.