Nijar : 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutum 6 A Diffa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31450-nijar_'yan_kunar_bakin_wake_sun_kashe_mutum_6_a_diffa
Hukumomi a Jamhuriya Nijar sun sanar da mutuwar mutane 6, da kuma raunanar wasu 37 a wasu jerin hare haren da wasu 'yan kunar bakin wake uku suka kai a jihar Diffa dake kudu maso gabashin kasar, kusa da kan iyakar Najeriya.
(last modified 2018-08-22T07:01:56+00:00 )
Jun 05, 2018 11:09 UTC
  • Nijar : 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutum 6 A Diffa

Hukumomi a Jamhuriya Nijar sun sanar da mutuwar mutane 6, da kuma raunanar wasu 37 a wasu jerin hare haren da wasu 'yan kunar bakin wake uku suka kai a jihar Diffa dake kudu maso gabashin kasar, kusa da kan iyakar Najeriya.

An dai kai hare haren ne a unguwar ''Diffa Kura'' dake birnin Diffa a cikin daren jiya Litini, a cewar wata sanarwa da ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar.

Sanarwar ta ce akwai kuma mutum 8 da suka samu munanen raunuka.

Mata biyu da namiji guda ne suka kai hare-haren, kuma duk sun hallaka.

Rahotanni sun ce an yi niyyar kai hare haren ne a makarantar Islamiyya.

Babu dai wata kungiya data dau alhakin kai hare haren, saidai sau tarin yawa akan danganta ire-iren wadanan ayyukan ta'adi ga kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram.

Shugaban kasar Isufu Mahamadu, ya yi tir da Allah wadai da harin, yana mai isar da ta'aziyya da fatan samun sauki ga wadanda lamarin ya rusa dasu.