'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 7 A Mozambique
'Yan sandar kasar Mozambique sun sanar da mutuwar mutum 7 sanadiyar harin 'yan bindiga a arewacin kasar
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto jami'an 'yan sandar kasar Mozambique na cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari yankin Macomia na jihar Cabo Delgado dake arewacin kasar inda suka kashe fararen hula 7 tare kuma da jikkata wasu 4 na daban.
Hukumar 'yan sandar kasar Mozambique din ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike domin gano wadanda suka kai wannan hari na baya-bayan nan wadanda ya sanya tsoro a zukatan mazauna yankin, har ta kai suna gudu daga yankin.
Majiyar labaran kasar Mozambique ta sanar da cewa daga watan Oktoban 2017 zuwa yanzu, 'yan tawayen sun kai hari kan wuraren bincike na jami'an 'yan sandar yankin da kuma sun kashe fararen hula da dama a yankuna da dama na jihar Cabo Delgado.