Kasar Habasha Ta Amince Da Sulhuntawa Da Makobciyarta Eriteria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31486-kasar_habasha_ta_amince_da_sulhuntawa_da_makobciyarta_eriteria
Gwamnatin kasar Ethiopia ko Habasha ta amince da sulhuntawa da makobciyar kasar Eriteria don kawo karshen yaye-yaken kan iyakan da kasashen biyu suka dade suna fafatawa a tsakaninsu.
(last modified 2018-08-22T07:01:56+00:00 )
Jun 06, 2018 14:38 UTC
  • Kasar Habasha Ta Amince Da Sulhuntawa Da Makobciyarta Eriteria

Gwamnatin kasar Ethiopia ko Habasha ta amince da sulhuntawa da makobciyar kasar Eriteria don kawo karshen yaye-yaken kan iyakan da kasashen biyu suka dade suna fafatawa a tsakaninsu.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar jam'iyya mai mulkin kasar ta Habasha tana fadar haka a yau Laraba, ta kuma kara da cewa ta amince da sulhuntawan ne, ba tare da wani sharidi ba, sannan ta amince da yerjejeniyar sulhun da ake kira "Sulhun Algeria" inda zata aiwatar da dukkan abubuwan da aka amince da su a cikin yerjejeniyar.

A bisa yerjejeniyan sulhu ta "Sulhun Algeria" wacce kasashen biyu suka rattabawa hannu a shekara ta 2000 a kasar Algeria, kasar Habasha za ta mikawa kasar Eriteria garin Bodam na kan iyaka sannan ta janye sojojin ta da ta jibge a kan iyakokin kasashen biyu. 

Kasashen Habasha da Eriteria sun fara sabani kan iyakokin kasashen biyu ne tun shekara ta 1998, sannan sun shiga yaki a tsakaninsu na tsawon shekaru biyu kafin a rattaba hannu kan yerjejeniyar sulhu ta "Sulhun Algeria"