Ethiopia Ta Karbi 'Yan Gudun Hijra Dubu 29
Kwamishinan koli dake kula da 'yan gudun hijra na MDD ya sanar da cewa cikin watani biyar na farkon wannan shekara ta 2018, kasar Ethiopia ta karbi 'yan gudun hijra sama da dubu 29
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya nakalto kwamishinan koli mai kula da 'yan gudun hijra na MDD cikin wani rahoto da ya fitar na cewa a cikin watani biyar na farkon wannan shekara ta 2018, 'yan gudun hijra dubu 29 da 211 suka shiga kasar Ethiopia, da hakan ya sanya adadin 'yan gudun hijrar dake cikin kasar ya kai dubu 920 da 262.
Rahoton na kwamishinan koli dake kula da 'yan gudun hijra na MDD ya sanar da cewa mafi yawan 'yan gudun hijrar dake cikin kasar Ethiopia sun fito ne daga kasashen da ake rikici da kuma yakin basasa.
Bayan kasar Ethiopia, kasar Uganda ce ta karfi mafi yawa daga 'yan gudun hijra na Nahiyar Afirka.