'Yan Boko Haram Sun Kashe Mutum 7 A Arewacin Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31580-'yan_boko_haram_sun_kashe_mutum_7_a_arewacin_kamaru
Kimanin mutane 7 ne suka rasa rayukansu sandiyar wani hari da mayakan kungiyar boko haram suka kai arewacin kasar kamaru.
(last modified 2018-08-22T07:01:57+00:00 )
Jun 10, 2018 02:27 UTC
  • 'Yan Boko Haram Sun Kashe Mutum 7 A Arewacin Kamaru

Kimanin mutane 7 ne suka rasa rayukansu sandiyar wani hari da mayakan kungiyar boko haram suka kai arewacin kasar kamaru.

Kamfanin dillancin labaran Meher ya habarta cewa a jiya asabar mayakan boko haram sun kai hari wasu kauyuka na arewacin kasar Kamaru tare da kashe fararen hula bakwai.

Tun daga lokacin da mayakan boko haram suka fara kai hare-haren ta'addanci a arewacin kamaru a shekaru 2015, yankunan arewaci da kuma arewa mai nisa sun  fuskanci hare-haren boko haram da dama.

Tun a shekarar 2009 ne kungiyar boko haram ta fara kai hare-haren ta'addanci a arewacin Najeriya, sannan a shekarar 2015, ta fadada kai hare-harenta zuwa kasashen Nijer, Tchadi da kuma arewacin Kamaru.

Kididdigar MDD ta ce rikicin ya hallaka sama da mutane dubu 20 sannan kuma ya raba wasu dama da miliyan biyu da mahalinsu.