Rikicin Kabilanci Ya Hallaka Mutum 10 A Kudancin Ethiopia
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31768-rikicin_kabilanci_ya_hallaka_mutum_10_a_kudancin_ethiopia
Shugaban ofishin sadarwa na yankunan kudancin Ethipia ya sanar da hallakar mutum 10 tare da jikkatar wasu da dama na daban sanadiyar rikicin kabilanci a kudancin kasar
(last modified 2018-08-22T07:01:59+00:00 )
Jun 16, 2018 14:34 UTC
  • Rikicin Kabilanci Ya Hallaka Mutum 10 A Kudancin Ethiopia

Shugaban ofishin sadarwa na yankunan kudancin Ethipia ya sanar da hallakar mutum 10 tare da jikkatar wasu da dama na daban sanadiyar rikicin kabilanci a kudancin kasar

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya nakalto Sulaimane Hailou shugaban ofishin sadarwa na yankunan kudanci wato Umamu-junubiya a kudancin kasar Ethipia na cewa rikicin kabilanci tsakanin kabilar Sidama da Wolaita da ya fara tun a ranar talatar da ta gabata,a garin Hawasa, zuwa yanzu ya ci rayukan mutum 10 tare kuma da jikkata wasu 89 na daban, sannan kuma ya raba wasu sama da 500 da mahalinsu.

Hailou ya kara da cewa ko baya ga wannan, rikicin ya yi sanadiyar rusa gidaje da dama tare kuma da kwashe dukiyoyin mutane a matsayin ganima.

Kabilun Sidama da Wolaita na daga cikin mahiman kabilu a kudancin kasar Ethiopia kuma tun da jimawa alaka tayi tsami a tsakanin wadannan kabilu dake zaune a jaha guda.

A nasa bangare, Daisy Daalaki shugaban jahar kudancin kasar ya ce sun dauki matakan da suka dace na dawo da zaman lafiya a garin na Hawasa.