Ivory Coast : Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 18
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31874-ivory_coast_ambaliyar_ruwa_ta_kashe_mutum_18
Rahoton tashar talabijin din France 24 ya ce A cikin birnin Abidjan na sami asarar rayuka da kuma ta dukiya.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 20, 2018 07:39 UTC
  • Ivory Coast : Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 18

Rahoton tashar talabijin din France 24 ya ce A cikin birnin Abidjan na sami asarar rayuka da kuma ta dukiya.

Rahoton ya ce babban birnin kasar Abidjan ya dade yana fama da matsalolin magudan ruwa wadanda har zuwa yanzu babu wani mataki da mahukunta suka dauka domin gyarawa.

Masu hasashen yanayi sun ce ci gaba da saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya na tsawon mako guda zai iya haddasa wani karin ambaliyar ruwan.

Gwamnatin kasar ta kira mazauna babban birnin kasar da su dauki matakan kare kawukansu daga fadawa cikin hatsari.