Mutum 10 Sun Mutu A Wurin Hakar Ma'adinai A Zambiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31894-mutum_10_sun_mutu_a_wurin_hakar_ma'adinai_a_zambiya
Mutane 10 ne aka tabbatar da mutuwarsu a yayinda wasu 10 kuma suka ji rauni sanadiyyar rubtawarwani wurin hakar ma'adinai a kasar Zambia a safiyar yau Laraba.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 20, 2018 14:28 UTC
  • Mutum 10 Sun Mutu A Wurin Hakar Ma'adinai A Zambiya

Mutane 10 ne aka tabbatar da mutuwarsu a yayinda wasu 10 kuma suka ji rauni sanadiyyar rubtawarwani wurin hakar ma'adinai a kasar Zambia a safiyar yau Laraba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar yansanda ta kasar Zambia na fadar haka a safiyar yau Laraba. Ta kuma kara da cewa hatsarin ya auku ne garin Kitwe da ke tazarar kilomita 400 daga birnin Lusaka babban birnin kasar. Girin yana cikin yankin da ake hakar jan karfe ko Copper a kasar.

Shugaban yansandan yankin da ake hakar Ma'adinai na kasar ta Zambia Chief Charity Katanga ya ce a cikin yan shekarun da suka gabata an dakatar da aikin hakar ma'adinai a wasu yankuna saboda irin wadannan hatsura.

Labrin ya kara da cewa gwamnatin kasar ta bada izini ga kananan kamfanin hakar ma'adinai na yankin, da su amfana da wasu wuraren hakar ma'adinai wadanda manya manyan kamfanoni suka bari don kyautata yanayin tattalin arzikin mutanen yankin da ake hakar ma'adinan. Sai dai don rashin kayakin aiki wani lokacin akan sami irin wadannan hatsura.

Kasar Zambia dai ita ce kasa ta biyu a duniya a yawan jan karfe ko Copper a halin yanzu.