An Karrama Sashen Hausa Na Radiyo Iran A Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32006-an_karrama_sashen_hausa_na_radiyo_iran_a_nijar
Kungiyar Marubuta ta kasa a Nijar #ASAUNIL ta karrama wasu gidajen kasa da kasa dake watsa shirye shiryen Hausa da lambar yabo bisa gudun muwar da suke bayar wa wajen bunkasa harsunan #Afirka musamman harshen Hausa.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 24, 2018 09:36 UTC
  • An Karrama Sashen Hausa Na Radiyo Iran A Nijar

Kungiyar Marubuta ta kasa a Nijar #ASAUNIL ta karrama wasu gidajen kasa da kasa dake watsa shirye shiryen Hausa da lambar yabo bisa gudun muwar da suke bayar wa wajen bunkasa harsunan #Afirka musamman harshen Hausa.

Sashen Hausa na Radiyon Iran ma ya samu irin wannan lambar yabo daga kungiyar #ASAUNIL.

Sauren gidajen radiyoyin sun hada da BBC, VOA, DW , RFI da CRI.

Wakiliyarmu a Yamai, babban birnin Jamhuriya Nijar, Nana Zainabu Amadu ce ta wakilci sashen Hausa na Radiyo Iran, wajen karbar lambar yabon.