Maroco Ta Mayar Da Alakar Diplomasiyarta Da Cuba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32143-maroco_ta_mayar_da_alakar_diplomasiyarta_da_cuba
Bayan kwashe shekaru 38, kasar Maroco ta mayar da alakar Diplomasiyarta da kasar Cuba
(last modified 2018-08-22T07:02:03+00:00 )
Jun 30, 2018 14:36 UTC
  • Maroco Ta Mayar Da Alakar Diplomasiyarta Da Cuba

Bayan kwashe shekaru 38, kasar Maroco ta mayar da alakar Diplomasiyarta da kasar Cuba

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto Bou Galib Al-atar sabon jakadan kasar Maroco a birnin Havana yana mika wasikar kama aikinsa ga shugaban kasar Cuba Miguel Díaz-Canel da hakan ke tabbatar da mayar da alakar diplomsiya tsakanin kasashen biyu.

A shekarar 1980 ne kasar Maroco ta yanke alakarta da kasar Cuba bayan ta zarge ta da taimaka wa kungiyar Polisario tare da amincewa da ita a matsayin kasa mai cin kashin kanta a shekarar 1976.

Rikici tsakanin gwamnatin Maroco da kungiyar Polisario ya fara ne a shekarar 1975, sannan a shekarar 1991, kasashen biyu sun cimma yarjejjeniyar tsagaita wuta bisa shiga tsakani da kuma sa ido na Majalisar Dinkin Duniya.