Shugaban Equatorial Guinea Ya Bada Umurnin Sakin Dukkanin Fursunonin Siyasar Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32211-shugaban_equatorial_guinea_ya_bada_umurnin_sakin_dukkanin_fursunonin_siyasar_kasar
Shugaban kasar Equatorial Guinea ya bada umurnin sakin dukkanin fursunonin siyasa da masu adawa da gwamnatin kasar daga gidan kurkuku.
(last modified 2018-08-22T07:02:04+00:00 )
Jul 06, 2018 02:12 UTC
  • Shugaban Equatorial Guinea Ya Bada Umurnin Sakin Dukkanin Fursunonin Siyasar Kasar

Shugaban kasar Equatorial Guinea ya bada umurnin sakin dukkanin fursunonin siyasa da masu adawa da gwamnatin kasar daga gidan kurkuku.

Shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema ya bada umurnin sakin dukkanin fursunonin siyasa da masu adawa da gwamnatinsa da ake tsare da su a gidajen kurkukun kasar da nufin samar da wata dama ta bai wa kowa 'yancin taka rawa a fagen siyasar kasar gami da bude zaman tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan adawa domin bunkasa ci gaban kasar.

Har ila yau shugaban Equatorial Guinea ya jaddada cewa: Gwamnatinsa zata gudanar da zaman tattaunawa da dukkanin bangarorin 'yan adawar kasar tare da ba su 'yancin bayyana ra'ayoyinsu karkashin sa-idon kungiyoyin kasa da kasa.

Shugaba Teodoro Obiang dan shekaru 76 a duniya ya dare kan karagar shugabancin kasar Equatorial Guinea ne tun a ranar 3 ga watan Agustan shekara ta 1979, kuma yana shirin gudanar da zaman taron kasa ne da nufin warware daambaruwar siyasar kasar tsakanin gwamnatinsa da 'yan adawa.