Shugaban Kasar Sudan Ya Tsawaita Tsagaita Bude Wuta Da Yan Tawayen Kasar
Shugaban kasar Sudan Umar Hassan EL-bashir ya bada sanarwan tsawaita tsagaita bude uta da yan tawayen kasar har na wasu watanni ukku.
Kamfanin dillancin labaran APF na kasar Faransa ya nakalto majiyar fadar shugaban kasar Sudan a birnin Khartun yana bada wannan sanarwan a jiya Alhamis. Labarin ya kara da cewa tsagaita bude wutan zai hada da yankunan Darfur, Kordofan da kuma yankin kogin nili mai shudin launi.
An fara tawaye na yankunan Kordofan da kuma kogin nilui ne jam kadan bayan bellewar sudan ta kudu daga kasar Sudan a shekara ta 2011.
Amma a yankin Darfur kabilun yankin wadanda ba larabawa ba sun sufa fafatawa da gwamnatin kasar ne tun shekara ta 2003 da nufin samun 'yenci daga kasar Sudan. Sai kuma a ranar 9 ga watan Maris da ya gabata na wannan shekara ta 2018 shugaban kasar ta Sudan Umar Hassan Albashir ya shelanta doka ta baci a wadannan yankuna ukku da ake da yan tawaye a ksar.