An Buda Ofishin Jakadancin Iritiriya A Adis Ababa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32350-an_buda_ofishin_jakadancin_iritiriya_a_adis_ababa
Bikin buda ofishin jakadancin kasar Iritiriya ya samu halartar shugaban kasar Isaias Afwerki da Firaministan Habasha Abiy Ahmed.
(last modified 2018-08-22T07:02:07+00:00 )
Jul 16, 2018 13:42 UTC
  • An Buda Ofishin Jakadancin Iritiriya A Adis Ababa

Bikin buda ofishin jakadancin kasar Iritiriya ya samu halartar shugaban kasar Isaias Afwerki da Firaministan Habasha Abiy Ahmed.

A yayin buda Ofishin jakadancin da ya gudana a jiya Lahadi, Shugaban Iritiriya Isaias Afwerki ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da yin aiki tukuru wajen ganin lamura sun ci gaba da tafiya lami lafiya tsakanin kasarsa da Habasha wadda suka daidaita tsakaninsu a makon da ya gabata.

Shugaban ya ce a halin da ake ciki kasashen biyu sun zama 'yan uwan juna don haka batun rikici tsakaninsu ya zama tarihi.

A nasa jawabin, mai masaukin baki Firaministan Habasha Abiy Ahmed jinjinawa hukumomin Iritiriya ya yi musamman ma shugaban kasar kan amincewa da shirin wanzar da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu, inda ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki tukuru wajen dorewar sabon kawance da bangarorin biyu suka kulla.

A shekarar 1993 ne kasar Iritiriya ta bayyana ballewarta daga kasar Habasha, inda a shekarar 1998 kasashen biyu suka shiga yaki na kan iyaka, lamarin da ya yi sanadiyar salwanta rayukan mutane akalla dubu 80, bayan shekaru biyu da yakin an cimma yarjejjeniyar sulhu, to sadai kasar Habasha tayi watsi da yarjejjeniyar inda ta bukaci a sake tattaunawa.