'Yan Ci-Rani 27 Sun Bace A Gabar Ruwan Murtaniya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32389-'yan_ci_rani_27_sun_bace_a_gabar_ruwan_murtaniya
Wani kwale-kwale mai dauke da 'yan ci-rani 102 ya tuntsire a gabar ruwan kasar Murtaniya.
(last modified 2018-08-22T07:02:07+00:00 )
Jul 19, 2018 07:55 UTC
  • 'Yan Ci-Rani 27 Sun Bace A Gabar Ruwan Murtaniya

Wani kwale-kwale mai dauke da 'yan ci-rani 102 ya tuntsire a gabar ruwan kasar Murtaniya.

Jirgin dai ya tuntsira ne a lokacin da yake kan hanyar zuwa kasar Spain a jiya laraba a kusa da garin Nouadhibou a yammacin kasar Murtaniya.

Kawo ya zuwa yanzu an tabbatar da bacewar mutane 27 sai dai an tseratar da wasu mutane 75. Kuma jami'an tsaro masu kula da gabar ruwan kasar ta Murtaniya tare da hadin gwiwar takwarorinsu na kasar Spain  suna ci gaba da ayyukan ceto domin gano sauran wadanda suka bace.

'Yan ci-rani da suke fitowa daga nahiyar Afirka suna mutuwa a cikin ruwa akan hanyarsu ta zuwa nahiyar turai.