Yajin Aikin Matukan Kamfanin Jiragen Sama Na Kasar Moroko
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32483-yajin_aikin_matukan_kamfanin_jiragen_sama_na_kasar_moroko
Kamfanin Jiragen sama na Royal Air Morroc ya dakatar da ayyukansa saboda yajin aikin da matukansa suke yi.
(last modified 2018-08-22T07:02:09+00:00 )
Jul 26, 2018 02:26 UTC
  • Yajin Aikin Matukan  Kamfanin Jiragen Sama Na Kasar Moroko

Kamfanin Jiragen sama na Royal Air Morroc ya dakatar da ayyukansa saboda yajin aikin da matukansa suke yi.

Kamfanin dillancin labaran Xinhua na kasar Sin ya ce; An dakatar da jigilar matafiya da ya kamata a yi daga kasar ta Moroko zuwa Tunisiya, Faransa da Spain.

Rashin jituwa a tsakanin matukan jirgin saman da kuma kamfani ta yi tsanani tun daga ranar Litinin bayan da su ka gudanar da wani zama wana ba kai ga cimma matsaya ba.

Matukan jirgin saman suna yin kuka ne akan rashin kyakkyawan albashi da kuma sauran hidimomi na rayuwa.