An Hana Wani Babban Dan Adawa A Kasar Congo Shiga Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32623-an_hana_wani_babban_dan_adawa_a_kasar_congo_shiga_kasar
Jami'an tsaron kan iyaka na kasar DMC Kongo sun hana Moise Katumbi hamshakin mai kudi kuma tsohon gwamnan lardin Katanga na kasar shiga kasarsa a jiya jumma'a.
(last modified 2018-08-22T07:02:12+00:00 )
Aug 04, 2018 07:16 UTC
  • An Hana Wani Babban Dan Adawa A Kasar Congo Shiga Kasar

Jami'an tsaron kan iyaka na kasar DMC Kongo sun hana Moise Katumbi hamshakin mai kudi kuma tsohon gwamnan lardin Katanga na kasar shiga kasarsa a jiya jumma'a.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto Katumbi yana fadar haka a shafinsa na tweeter, ya kuma kara da cewa gwamnatin kasarsa ta hana shi tafiya zuwa kasar da jirgin sama kuma ta hana shi shiga kasar daga kasar Zambia a jiya jumma;a/

Moise Katumbi ya ce yana son isa kasar kafin 8 ga watan Augusta don shigar da takardunsa na neman takarar shugabancin kasar wanda za'a gudanar a karshen wannana shekara.

Katumbi yana gudun hijiran radin kansa a kasashen waje tun shekara ta 2016 bayan da aka zarge shi da an-mundaha da kuma wasu laifuffuak. 

Jami'an tsaron kasar Congo sun bayyana cewa za'a kama shi idan ya taka kasar.