Cutar Ebola Ta Hallaka Mutum 33 A Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32632-cutar_ebola_ta_hallaka_mutum_33_a_congo
Ma'aikatar lafiya ta kasar Demokaradiyar Congo ta sanar da mutuwar mutum 33 sanadiyar kamuwar da cutar Ebola a gabashin kasar
(last modified 2018-08-22T07:02:12+00:00 )
Aug 05, 2018 03:09 UTC
  • Cutar Ebola Ta Hallaka Mutum 33 A Congo

Ma'aikatar lafiya ta kasar Demokaradiyar Congo ta sanar da mutuwar mutum 33 sanadiyar kamuwar da cutar Ebola a gabashin kasar

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto ma'aikatar lafiya ta jamhoriyar Demokadariyar Congo a jiya asabar na cewa cutar ebola ta yi sanadiyar hallakar mutum 33, kuma a halin da ake ciki akwai wasu 13 na daban dake dauke da wannan cuta.

Idan ba a manta ba dai a ranar 8 ga watan Mayun da ya gabata ne cutar Ebola ta sake bulla a garin Bikoro na jihar Équateur dake arewa maso gabashin kasar Congon, daga nan kuma cutar ta wanzu zuwa garin Mbandaka, makuni biyu da bayyana karshen cutar, a makon jiya cutar ta sake bulla a garin Beni na gabashin kasar, da ya zuwa yanzu ta ci rayukan mutum 33.

Daga shekarar 2013 zuwa 2016 cutar ebola ta ci rayukan mutum sama da dubu 11 da 300 a yammacin kasashen Afirka.