An Hallaka Wasu 'Yan Bindiga 4 A Burundi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32635-an_hallaka_wasu_'yan_bindiga_4_a_burundi
Dakarun tsaron Burundi sun sanar da hallaka wasu 'yan bindiga 4 da ake zargin 'yan fashi da makami a kasar
(last modified 2018-08-22T07:02:12+00:00 )
Aug 05, 2018 03:14 UTC
  • An Hallaka Wasu 'Yan Bindiga 4 A Burundi

Dakarun tsaron Burundi sun sanar da hallaka wasu 'yan bindiga 4 da ake zargin 'yan fashi da makami a kasar

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya nakalto wani jami'in kasar Burundi na cewa a daren jiya asabar jami'an tsaron kasar sun yi arangama da wasu 'yan bindiga 4 da ake zaton 'yan fashi da makami a Bujunbura babban birnin kasar tare da hallaka su.

Rahoton ya ce 'yan bindigar sun abkawa wata babbar Kasuwa  ce dake babbar birnin kasar, tare da fille kan wani mutum da ya shiga kasuwar domin sayayya, bayan wani ta'addanci ne, jami'an tsaron suka kai farmaki, inda suka hallaka 'yan bindigar gaba daya.

Kasar Burundin dai ta shiga cikin rudani ne tun bayan da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya sanar da aniyarsa ta yin tazarce a kan karagar mulkin kasar a karo na uku a 2015 lamarin da 'yan adawa suka ce ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.