Gwamnatin Habasha Ta Sulhunta Da "Yan tawaye
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32673-gwamnatin_habasha_ta_sulhunta_da_yan_tawaye
A jiya talata ne talabijin din gwamnatin kasar Habasha ta sanar da cewa an cimma matsaya akan yin sulhu da 'yan tawayen yankin Aromo wanda a baya gwamnatin kasar take daukarsu a matsayin 'yan ta'adda
(last modified 2018-08-22T07:02:13+00:00 )
Aug 08, 2018 03:02 UTC
  • Gwamnatin Habasha Ta Sulhunta Da

A jiya talata ne talabijin din gwamnatin kasar Habasha ta sanar da cewa an cimma matsaya akan yin sulhu da 'yan tawayen yankin Aromo wanda a baya gwamnatin kasar take daukarsu a matsayin 'yan ta'adda

Gwamnatin kasar Habasha a karkashin Firma minista Abi Ahmad Ali ta fito da shirin sulhunta al'ummar kasar da kawar da sabani da take da shi da kasar Eriteria.

A wannan makon da ake ciki, gwamnatin kasar ta ba da dama ga wasu shugabannin musulmi da suke gudun hijira su ka koma gida.

A siyasar yankin, kasar ta Habasha ta bude sabon shafi a alakarta da kasar Eritrea bayan shekaru ashirin na zaman tsama a tsakaninsu.

Fira ministan kasar ta Habasha Abi ya zargi Hadaddiyar Daular Larabawa da hannu a cikin yake-yaken da su ke faruwa a yanki, da kuma wasu kasashen yammacin Afirka.