Kungiyar ECOWAS Ta Bukaci Zaman Tattaunawa Tsakanin Bangarorin Siyasar Kasar Togo
Shugaban kwamitin zartarwar kungiyar bunkasa harkar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ya bukaci bangarorin siyasar kasar Togo da su dauki matakin warware rikicin siyasar kasar ta hanyar lumana.
A ganawarsa da bangaren 'yan adawar siyasar kasar Togo a daren jiya Alhamis a birnin Lome fadar mulkin kasar: Shugaban kwamitin zartarwar kungiyar bunkasa harkar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS Jean Claude Brou ya jaddada muhimmancin gudanar da zaman tattaunawa tsakanin gwamnatin Togo da gungun 'yan adawar kasar da nufin neman hanyar warware dukkanin matsalolin da suke addabar kasar musamman harkokin siyasa.
Jean Claude Brou ya jaddada cewa: Fahimtar juna a tsakanin gwamnatin Togo da 'yan adawar kasar zai taimaka gaya a fagen aiwatar da taswirar hanya da aka cimma a kasar a ranar 31 ga watan Yulin wannan shekara da ta kunshi aiwatar da gyarar fuska a kundin tsarin mulkin kasar da harkokin tafiyar da gwamnati gami da share fagen gudanar da zabukan 'yan majalisun Dokokin Kasar a ranar 20 ga watan Disamban wannan shekara ta 2018.