An Haramta Kayayyakin Amurka A Senegal
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32768-an_haramta_kayayyakin_amurka_a_senegal
Domin goyon bayan kasar Turkiya, Al'ummar kasar Senegal sun haramta sayar kayayyakin da suke fitowa daga kasar Amurka.
(last modified 2018-08-22T07:02:15+00:00 )
Aug 15, 2018 02:10 UTC
  • An Haramta Kayayyakin Amurka A Senegal

Domin goyon bayan kasar Turkiya, Al'ummar kasar Senegal sun haramta sayar kayayyakin da suke fitowa daga kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa Al'ummar kasar Senegal sun fara farfagandar haramta amfani da kayayyakin da suke fitowa daga kasar Amurka domin kawo goyon bayansu ga kasar Turkiya na kalubalartar takunkumin da Amurka ta kakaba mata.

Wasu kungiyoyin farar hula ne na kasar suka shelanta  wannan farfaganda, inda suka fitar da sunayen kayayyaki kirar kasar Turkiya suka kuma 'yan kasar da su dinga aikin da wadannan kayayyaki a maimakon aiki da na kasar Amurka

Tuni dai wannan farfaganda ya fara samun karbuwa daga wasu 'yan kasar ta Senegal, inda tuni suka haramta amfani da kayayyakin na Amurka.

A ranar 1 ga watan Augusta ne kasar Amurka ta kakabawa wasu ministoci biyu na kasar Turkiya biyo bayan kudirin da mahukuntan Turkiyan suka dauka na rkin sakin malimin kiristan nan Andrew Brunson dan kasar Amurka da aka kama shi da hannu dumu-dumu a yunkurin juyin milkin kasar ta Turkiya.