Abu Ghaid Ya Zargi Iran Da Tsoma Baki A Harakokin Kasashen Larabawa.
Babban Saktaren kungiyar kasashen Larabawa ya zargi kasar Iran da yin katsa landan a harkokin kasashen Larabawa, tare da bayyana Iran a matsayin barazana ga harakokin tsaron kasashen Larabawa.
Kamfanin dillancin labaran Fars ya nakalto Ahmad Ghaid yayin ganawarsa da shugaban kasar Yemen mai murabus Abdu Rabahu Manssor Hadi jiya Talata a birnin Alkahra na da'awar cewa kasar Iran na bayan tayar da hargizi ne a kasar Yemen da kuma dagula al'amuran tsaro a hanyar jiragen ruwan dakon man fetir na tekun maliya.
Wannan firici na babban saktare kungiyar Larabawa na zuwa ne bayan da dakarun tsaron Yemen da mayakan sa kai na kungiyar Ansarullah suka halba makami mai Linzami kan wani jirgin ruwan dakon Man da Saudiya a ranar 25 ga wata yunin da ya gabata a gabar tekun ruwan Alhudaida.
Duk da killacewar da kawancen saudiya ya yiwa kasar Yemen, ama ko wata rana karfin dakarun kasar ta Yemen na kara karuwa.
Sama da shekaru uku kenan da kasar Saudiya bisa goyon hadaddiyar daular larabawa, Amurka da wasu kasashen Larabawa ke kai hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar kasar Yemen, amma har yanzu sun kasa cimma manufofinsu.